Bata-gari sun caccaka wa malamin Jami’ar BUK wuka, sun bukaci ya ‘basu albashinsa’

Karatun minti 1

Wasu bata-gari dauke da makamai sun haura gidan wani malami mai suna Hussani da ke sashin koyar da aikin kula da marasa lafiya na  jami’ar Bayero da ke Kano. Rahotanni sun bayyan cewa mutanen sun caccaka masa wuka, kamar yadda Sahelian Times ta rawaito.

Bata-garin sun kuma kwace musu wayoyi, mukullin motarsa da wasu kudade.

Da yake shaida wa jaridar, wani makusancin malamin ya ce bata-gari sun shiga gidan malamin da ke unguwar Shagari Quaters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano da misalin karfe 3 na dare. Ya shaida cewa sun caccaka masa wukar a kirginsa da baya.

Kazalika malamin ya samu munanan yanka a saman goshinsa da fuskarshi tare da yi wa matarsa dukan kawo wuka, abinda ya kai ga ji mata ciwo.

Jaridar ta rawaici cewa, bata-garin sun afka masa ne da nufin cewar sai ya basu kasonsa daga cikin albashi da alawus dinsa da suka ce gwamnatin Najeriya ta biya su.

Sai dai amsar da Malam Hussaini ya basu na cewa ba hi da kudin da zai ba su, lamarin da ya sa suka hasala suka kuma afka masa tare da matar ta shi da matsanancin fushi.

Makusancin malamin ya ce sun yi kokarin tafiya da motar malamin, sai dai sun samu tasgado, abin da ya tilasta su ka bar ta, su ka kuma yi kokarin kashe shi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog