Ganduje ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Kwankwaso kan rasuwar mahaifinsa

Karatun minti 1
Gwamna Abdullahi Ganduje -APC

Gwamnatin jihar Kano tare da gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje sun mika sakon ta’aziyyarsu ga tsohon gwamnan jihar Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso kan rasuwar mahaifinsa.

Ranar Alhamis dai mahaifin Engr Kwankwaso kuma Majidadin Kano/Makaman Karaye, Alhaji Musa Sale Kwankwaso, ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

A cikin wata sanarwa da Kwaishinan yada labaran Kano, Mallam Muhammad Garba ya fitar, ya ce gwamnatin Kano da gwamna Ganduje sun nuna kaduwarsu ga mutuwar mahaifin Kwankwaso, wanda suka bayyana a matsayin mutum nagartacce kuma jajirtacce mai kishin al’ummarsa.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar tana mika sakon ta’aziyya zuwa tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabiu Musa Kwankwaso da dukkani iyalansa.

Kwamishinan ya rawaito gwamnan yana cewa; “A madadi na da iyalai na, Gwamnatin jihar Kano da al’ummar Kano baki daya, Ina mika sakon ta’aziyyata ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Masarautar Karaye da dukkanin al’ummar yankin bisa rasuwar daya daga cikin masu nadin Sarki wanda ya kasance shugaban Madobi na sama da shekaru 20.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog