Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Atiku ya yi Allah wadai da kamun Abu Hanifa Dadiyata ‘dan Kwankwasiyya

2 min read

Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadinshi na yacce gwamnatin Najeriya take kama ‘yan gwagwarmaya da sunan garkuwa da su.

DABO FM ta binciko cewar; Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, a ranar Asabar, 3 ga watan Agusuta.

Atiku Abubakar yayi nuni da cewa; ‘Yancin fadar albarkacin baki ya wuce kudin tsarin mulki kasa, shine ginshikin tabbatuwar Dimokradiyyarmu.

“Munyi Allah wadai da wannan kamen mutanen da akeyi da sunan anyi garkuwa dasu.”

Atiku yayi kira da bangaren shari’a na kasa da shigo cikin lamarin domin ceto Najeriya daga mulkin kama karya.

Hakan na zuwa ne bayan da ake zargin gwamnatin Najeriya da kama wasu ‘yan gwagwarmaya dake adawa da gwamnatin APC a cikin makon farkon wata Agusta.

DABO FM ta binciko cewa; Da safiyar ranar Asabar ne dai akayi awon gaba da matashinnan dan takarar shugabancin kasa a jami’iyyar AAC, Omoyere Sowore a gidanshi bayan yunkuri na fitowa zanga-zanga akan nuna rashin goyon bayan yacce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari take tafiyar da mulkinta.

Haka ma a daya bangaren, an nemi dan gwagwarmaya Abu Hanifa Dadiyata, mai kare muradin Kwankwasiyya a kafofin sadarwa jim kadan bayan shigewarshi gida a garin Kaduna. An alakanta dauke ga gwamnati bisa amfani da jami’an DSS.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.