Labarai

Atiku ya yi Allah wadai da kame-kamen ‘Yan gwagwarmayar siyasa da gwamnatin Buhari take yi

Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadinshi na yacce gwamnatin Najeriya take kama ‘yan gwagwarmaya da sunan garkuwa da su.

Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, a ranar Asabar, 3 ga watan Agusuta.

Atiku Abubakar yayi nuni da cewa; ‘Yancin fadar albarkacin baki ya wuce kudin tsarin mulki kasa, shine ginshikin tabbatuwar Dimokradiyyarmu.

“Munyi Allah wadai da wannan kamen mutanen da akeyi da sunan anyi garkuwa dasu.”

Atiku yayi kira da bangaren shari’a na kasa da shigo cikin lamarin domin ceto Najeriya daga mulkin kama karya.

Hakan na zuwa ne bayan da ake zargin gwamnatin Najeriya da kama wasu ‘yan gwagwarmaya dake adawa da gwamnatin APC a cikin makon farkon wata Agusta.

DABO FM ta binciko cewa; Da safiyar ranar Asabar ne dai akayi awon gaba da matashinnan dan takarar shugabancin kasa a jami’iyyar AAC, Omoyere Sowore a gidanshi bayan yunkuri na fitowa zanga-zanga akan nuna rashin goyon bayan yacce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari take tafiyar da mulkinta.

Haka ma a daya bangaren, an nemi dan gwagwarmaya Abu Hanifa Dadiyata, mai kare muradin Kwankwasiyya a kafofin sadarwa jim kadan bayan shigewarshi gida a garin Kaduna. An alakanta dauke ga gwamnati bisa amfani da jami’an DSS.

Karin Labarai

Masu Alaka

Mutane sun fara suma, kafin zuwan Kwankwaso da Atiku filin Sani Abacha

Dabo Online

Na’urar tattara zabe ta INEC ta nuna Atiku ne ya lashe zaben 2019 – PDP

Dabo Online

2023: PDP ta shiga neman sabon dan takarar shugabancin kasa da zata tisa a gaba

Muhammad Isma’il Makama

Atiku bazai taba nasara ba – Na hannun daman Atiku

Dabo Online

Ban amince da zaben 2019 ba, kuma sai na kai kotu

Dabo Online

Atiku bai je Amurka ba – Paul Ibe

Dabo Online
UA-131299779-2