Home LabaraiFintiri ya soke biyan kudin makaranta a Adamawa, ya dawo da shirin ciyarwa a Makarantu

Fintiri ya soke biyan kudin makaranta a Adamawa, ya dawo da shirin ciyarwa a Makarantu

by Dabo Online
0 comments

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiti ya bayyana shirin yin karatun kyauta a jiihar domin samuwar Ilimi ga dukkanin ‘yan Adamawa musamman wadanda iyayensu basu da karfin biya musu kudaden karatun.

Fintiri ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ‘yan jami’iyyar ADC wanda dan takarar gwamna a jami’iyyar Sanata Abdulazeez Iyako yake jagoranta suka kai masa fadar gwamnatin jihar dake garin Yola.

Gwamnan yace shirin zai fara aiki ne a watan Satumbar 2019, tare da bayyana makasudin yin shirin shine samarwa da ‘yayan talakawa Ilimi wadanda a baya suka rasa damar yin karatu.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinshi ta shirya tsaf wajen gyaran makarantun gwamnati a jihar domin suyi gogayya da makarantu masu zaman kansu dake jihar.

“Tsarinmu shine mu fara mayar da ingancin makarantun gwamnati sunyi gogayya da makaratu masu zaman kansu. Zamu kuma dawo da dukkanin filayen makaratu da aka rabawa wasu mutane.” – Gwamna Fintiri.

Yace “ba kamar a baya ba, a yanzu dalibai suna karbar abinci sau 3 a kowacce rana ba tare da biyan ko kobo ba.

DABO FM ta rawaito cewa gwamna Fintiri ya kara da cewa; gwamnatinshi ta farfado da shirin ciyarwa a makarantu sakandire na kwana da suke jihar, inda yanzu shirin ya fara da makarantu tara, ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba, shirin ciyarwar zai zaga dukkanin makarantun kwana 65 da suke fadin jihar.

Students of Government Girls College, Yola, get ready for breakfast
Daliban a lokacin da suke karbar Abinci.
Hoton Daily Trust.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00