(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Batanci ga Annabi: Kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mawaki

Karatun minti 1

Babbar kotun shari’ar musulinci dake Hausawa Filin Hockey a jihar Kano ta yankewa wani matshi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Rahoton DABO FM ya bayyana alkalin kotun Khadi Aliyu Muhammad Kani ya zartar da hukuncin a ranar Litinin bayan samun Yahaya Aminu Sharif da laifin.

Sharif wanda ke zaune a unguwar Sharifai cikin kwaryar birnin Kano ya yi wakar dake dauke da cin zarafin Fiyayyen halittu a watan Maris wanda ya yada ta ta cikin manhajar sada zumunta ta Whatsapp.

Biyo bayan hakan masu zanga-zanga suka bankawa gidansu shi mai batancin wuta, suka kuma kai kara zuwa hukuma babban ofishin hukumar Hisba. Kamar yadda KANOFUCUS ta fitar.

Haka kuma wannan kotu ta yankewa wani mai suna Umar Farouq dan unguwar Sharada dake Kano hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari biyo bayan kalaman izgili ga Allah subahanahu wa ta’ala.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog