An kuma yanke wa wani da ya yiwa Allah SWA izgili shekaru 10 a gidan yari

dakikun karantawa

Bayan yanke wa wani mawaki hukuncin kisa ta hanyar rataya, babbar kotun shari’ar musulinci ta yanke wa wani mutum shekaru 10 a gidan kaso bayan yiwa Ubangiji izgili a bainar jama’a.

Rahoton DABO FM ya bayyana mutumin mai suna Umar Faruk dake unguwar Sharada a birnin Kano yayi izgili ga Allah SWA lokacin da suke tsaka da jayayya a bainar jama’a.

Idan baku manta ba a ranar 1 ga Afrilun 2020, DABO FM ta kawo muku rahoton shima wani matshi da aka zarga da yin irin wannan batanci a unguwar Dabai dake karamar Hukumar Dala, wanda har ta kai ga masu zanga-zanga a unguwar sun rushe gidan da yake.

Bayan rushe gidan washe gari wasu masu kare wanda ya yi batancin suka dawo unguwar ta Dabai domin daukar fansa wajen makota, wanda har takai ga anyi dauki ba dadi da ‘yan wannan unguwa suka fatattaki magoya bayan wancen matshi da aka zarga dayin batanci ga fiyayyen halittu.

A wancen karon dai dai lokacin da muke tattaunawa da Dagacin unguwar Dabai, Malam Sunusi Yallabai akan al’amarin, sai aka kawo masa rahotan yadda wasu mutane sukazo a motoci guda 2 da babura masu tarin yawa.

An tabbatarwa da dagaci cewa “sunzo ne domin su dau fansar rushe gidan da akayi wa dan uwansu.”

Wasu shaidun ido da muka samu adaidai lokacin da abin ya faru sun bayanawa DABO FM cewar mutanen sunzo ne domin su tayar musu da hankali, suna zikiri, sunata zage-zage.

“Sun taho suna Zikiri, suna ta zage-zage, tin jiya muke ta wannan rigimar kokarin kwantar da tarzoma, su kuma sunzo suna ta kokarin su kuma tayar mana da rigima.”

“Sun zo a mota guda biyu da babura masu yawa sosai, sunzo mana tashin hankali, suna neman su sa mutanen gari su biye musu ayi rigima.”

“Motocin kirar Honda Odyssey da Honda Panadol Extra da baburan Roba-Roba da Karfe-Karfe.”

Sai dai sun bayyana mana cewar mutanen dake wajen sun yi kokarin korarsu tare da tsoran da sukaji na cewar jami’an yan sanda suna kan hanyarsu ta zuwa, kamar yadda zaku gani a bidiyon kasa.

Shugaban bijilanti na wannan shiya, Babalili Abdullahi ya tabbatar mana da afkuwar wannan abu tare da kokari da jami’an tsaro suka yi wajen dakile wannan balahira.

Zuwa yanzu dai babu wani tabbaci na hukunta wannan matashi da aka zarga da batanci ga Annabi SAW wanda ke zaune a unguwar Dabai dake karamar hukumar Dala cikin birnin Kano.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog