(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

BBC HAUSA ta gargadi shafukan dake amfani da sunanta wajen yada labaran karya

Karatun minti 1

Daga shafin BBC Hausa

A yakin da BBC ta ke yi da yada labaran boge, kafar ta gano wani shafi da aka bude da sunan ”Bbc hausa nigeria” a shafin Facebook inda shafin ke karkatar da hankulan jama’a zuwa ga labarun karya da sunan kafar BBC Hausa.

Akwai irin wadannan shafukan a kafafen sada zumunta na Intanet da dama, masu yada labaran karya da sunan BBC Hausa.

Wani labari da irin wadannan shafuka na boge suka buga shi ne labarin da aka alakanta sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso yana zagin wasu ‘yan siyasa da masu sarauta na jihar Kano.

Sunan shafin bogin dake yada labaran karya da sunan BBC HAUSA

BBC Hausa ta nisanta kanta daga wannan labarin da kuma makamantansu a irin wadannan shafukan na boge.

Daga shafin BBC ta manhajar Twitter.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog