Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin tituna da rijiyoyin burtsate a guraren da za’a sake zabe

A daren jiya Juma’a 15/03/19, gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Dr Abdullahi Ganduje ta kaddamar da fara aikin titi a mazabar Gama dake karamar hukumar Nassarawa.

Sabon Titin unguwar Gama, Brigade a karamar hukumar Nassarawa.

Al’ummar wannan yanki sun tashi da ganin manyan motocin tituna da kuma na haka rijiyar burtsate.

Bayan dan buncike da muka gudanar, mun gano cewa gwamnatin na da bukatar gina rijiyoyin burtsatsen sama da guda 40 a cikin mako guda.

Mazabar Gama na daya daga cikin mazabun da za’a sake gudanar da zaben gwamna a fadin jihar Kano, mazabar da tafi kowacce mazaba girman masu kada kuri’a a cikin jerin mazabun da za’a sake gudanar da zaben.

Duk a sabon titina na Gama

Sai dai bisa dukkan alamu, al’umnar yankin dama masu amfani da shafukan sada zumunta musamman na Facebook, sun baiwa titin sunan ABBA GIDA GIDA ROAD.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.