Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sha kashi a hannun takwararta ta Wolverhamptom Wanderers da ci 2 – 1.
Wasan da aka buga a daren yau Asabar 16/03/19 a filin wasa na Molineux na kasar Ingila.
Dan wasa Raul Jimenez na Wanderers ne ya samu nasarar jefa kwallon farko a minti na 70, yayin da bayan mintuna 6 ne dan wasa Diogo Jota ta jefawa Wanderers kwallo ta 2.
A minti na 90, matashin dan wasa na kasar Ingila, Marcus Rashford ya jefa kwallon farkiya ga kungiyar ta United.
Wasan ya nuna cewa anyi waje da kungiyar ta United a gasar kofin FA.
Daga daya bangaren kuwa, Manchester City ta lallasa takwarta ta Swansea ta ci 3-2, wanda hakan ya bata damar matsawa matakin gaba a cikin gasar.