(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Boye Tallafin Korona: Buhari ne da babban laifi, cewar Mu’azu Magaji WIN-WIN

Karatun minti 1
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya

Engr Mu’azu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na jihar Kano ya daura alhakin boye kayan Tallafin Korona da wasu gwamnoni su ka yi a kan Shugaba Muhammadu Buhari.

DABO FM ta tattara cewa a kalla jihohi 9 ne wasu da ba a san ko suwaye ba suke fasa rumbunan ajiyar abinci na daga tallafin cutar Korona.

Jihohin sun hada da Adamawa, Edo, Ekiti, Kwara, Osun, Ogun, Kwara, Kaduna, Legas, Pilato da jihar Taraba.

Engr Mu’azu ya ce laifin Gwamnoni kadai shi ne sun ki raba kayan abincin, inda ya ce babban mai laifi shi ne shugaba Muhammadu Buhari da bai yi kadi ya ga yadda aka yi rabon kayan ba.

“Laifin Gwamnoni shi ne sun ajiye sun ki rabawa, amma babban laifin Buhari shi ne rashin bin sahu, rashin dan kunne in ba a aiwatar da umarni ba.

“Shugabanci ai sai da bin diddigi da jan kunne kai har ma da horo idan ba a yi daidai ba.”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog