‘Yan sanda sun kama wani Boka da yake sa matasa su kawo masa idon jarirai a Kano

dakikun karantawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani Boka da ake zarginsa da neman matasa su kawo masa idanuwar jarirai domin yayi tsafi da su a unguwar Hotoro ta birnin jihar Kano.

An zargi mutumin mai suna Yahaya da juyar da hankalin wani matashi mai suna Kabiru Sani  mai shekara 23, lamarin da ya sanya yake bin umarnin duk abinda bokan ya saka shi.

Matashin ya ce, ya je wajen Yahaya ne domin ya bashi magani a kan wata cuta da take damunsa, a nan ne bokan ya bashi wasu turarruka da maganin da zai hada da fitsarinsa ya sha.

“Na zo wajen Yahaya a kan bani da lafiya zai taimaka min, sai ya dauki garin magani da wani ruwa ya bani, ya ce min nayi amfani da fitsarina zuwa kwana 3. Da na dawo sai ya bani rubutu na kwana 3 ya bani turare, shikenan hankali na ya juye.”

“Duk abinda ya ce min shi nake yi.  Daga nan shikenan yake cemin zai bani miliyan 1, daga karshe ya ce min in kawo yaro jinina za a cire idonsa zai yi wa wani soja layar bata. Na samo yaron dan gidan yayata ne, shi ne naje na samu yayar tawa nake fada ga abinda Mallam yace.”

Hankalinta ya tashi, ni ma naji jikina duk wani iri shi ne muka zo ofisihin ‘yan sanda don mu kawo korafi.”

Rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun kakakinta, DSP Haruna Kiyawa ya tabbatar da kamun wanda ake zargi.

“Sunansa Yahaya a unguwar Hotoro,  mun kamo shi a nan Shedikwatar ‘yan sanda a nan Bompai bayan korafi a kansa. Ya nemi wani matashi bayan ya juyar da kansa a kan ya kawo masa idon jariri jininsa.

“Ana kokarin samu idon yaro ne muka kawo sa.”

A yayin kamun, DSP Haruna ya ce sun kama Yahaya tare da layu, kwarya, kasa, carbi, farin kyalle na likkafani, Jan turare a kwalba, Jan kyalle, wani abu daga jikin dabba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog