(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
/

Buhari yana ingiza wutar yaƙin basasa a Najeriya – Kperogi

Karatun minti 1
Shugaba Buhari ya gaza
Shugaba Muhammadu Buhari

Faruk Adamu Kperogi, ɗaya daga fitattun tsofaffin ‘yan jarida a Najeriya ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana ingiza wutar yakin basasa kasar.

Kperogi, yanzu haka malami a sashin koyar da aikin jarida na jami’ar Kennesaw State University da ke birnin Georgia a ƙasar Amurka, ya ce tsarin da gwamnatin ta dauka wajen rubuce-rubucenta yana nuna ta ɗauki bangare a rikicin da ke faruwa tsakanin Fulani da Yarabawa.

A wata muƙala da ya fitar a watan Janairu, ya ce ya kamata gwamnatin Buhari ta yi tunanin cewa sai da ƙasa fa sannan a ke yin mulki.

Ya ce kuma “Ƙasa ba za ta tabbatar da tsayuwar kasa ba ta hanyar tashin hankali da kuma nuna goyon bayan wata ƙabila fili tare da rashin iya bambamce ‘yan ba ruwana idan ana rikici.

Ya ƙara da cewa “duk gwamnatin da ta san me ta ke yi, ta na ƙoƙari ne wajen zama yar tsakiya duk lokacin da a ke rikici.”

“A muƙalata ta baya na nuna fargabar kasancewar Buhari a matsayin wanda zai kashe Najeriya, kuma yanzu yana yin abubuwan da suke tabbatar da maganata.”

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog