(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

A Gaggauce: Ganduje ya sanya wurin da za a yi muhawara tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da wurin da za a zauna domin tsefe aya daga tsakuwa tsakanin malaman jihar Kano da Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara.

Tin dai a makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta haramta wa malamin yin wa’azi tare da rufe masallatansa a faɗin jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya ce za a gudanar da muhawarar ne a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, kamar yadda ya bayyana wa sashin Hausa na Muryar Amurka cikin wata tattaunawa.

Gwamnan ya ce an amince da yin muhawarar a fadar sakamakon tarihin da fadar ta ke da shi na saba gudanar da muhawara kan addini.

“Mun yadda za a yi muhawar kamar yadda Sheikh Abduljabbar ya buƙata kuma bayan ya yi magana da wasu malamai a jihar waɗanɗa duka suka amince.”

Sai dai har yanzu bai bayyana rana da lokacin da za a tafka muhawarar ba, ya ce gwamnatin tana jiran malaman jihar ne domin su kammala shiryawa.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Abba Anwar ya ce gwamnatin ta bai wa malaman jihar na kowane bangare mako biyu domin shirya zaman muhawarar.

Gwamnan ya ƙara da cewar, bude masallacin malamin da cigaba da wa’azinsa ya alakantu da binciken jami’an tsaro.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog