Labarai

Buhari zai ciwo bashin dalar Amurka miliyan 890 domin yaki da sauro

Gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala miliyan 890 daga asusun duniya domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.

Majiyar Dabo FM ta bayyana gwamnati ta ce za ta kashe wadannan kudade wajen yaki da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da tarin fuka daga shekarar 2021 zuwa 2023. Kamar yadda jaridar PremiumTimes ta rawaito.

Shugaban kwamitin sa ido kan tallafin da asusun duniya ke bai wa Najeriya (CCM) Dozie Ezechukwu ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.

Ezechukwu ya ce bisa ga kason kudaden da gwamnati ta yi zazzabin cizon sauro zai dauki babban kaso daga cikin wadannan kudade da ya kai dala miliyan 417, kanjmau, dala miliyan 329 sannan tarin fuka dala miliyan 143.

Ya kara da cewa gwamnati ta tsara matakan da za su taimaka mata wajen kashe wadannan kudade yadda ya kamata ba tare da wani ko wasu sun yi sama da fadi da su ba.

Masu Alaka

Tsaro: Ka daina wasa da hankalin ‘yan Najeriya -Kungiyoyin kare hakkin dan adam ga Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Ba ƙaramin namijin ƙoƙari nake wajen mulkar Najeriya ba tare da ta wargaje ba -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan ginin sabon filin tashin Jirage a jihar Ebonyi

Dangalan Muhammad Aliyu

Gwamnati Najeriya ta sheka ‘Al-Kazzibu’ akan ceto daliban ABU guda 3 – Dangin daliban

Dabo Online

Yaki da cin Hanci da Rashawa a Najeriya Siyasa ce da daukar fansa kawai – Farfesa

Dabo Online

Gwamnatin tarayya zata fara rabawa ‘yan Zamfara N5000 a kowanne wata – CCT

Dabo Online
UA-131299779-2