El Rufa’i
Labarai

El-Rufa’i yayi tir da kashe Tiriliyan 17 a gyaran wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koka kan yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe naira Tiriliyan 1.7 a harkar wutan lantarkin kasar nan sannan har yanzu ana cikin duhu a kasar.

Majiyar Dabo FM ta ruwaito El-Rufai ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci gaba da narka wadannan makudan kudade ba a abinda kiri-kiri ba samun sakamako mai kyau ake yi ba. Sannan ya roki mutane da su kara hakuri zuwa lokacin da kwamitin sa zata kammala bincike akan wannan sashe fin su ce wani abu.

” Gaba da maganar wutan lantarki a kasar nan ya tabarbare matuka. Tun daga yadda ake biyan kudin wutan da ake sha zuwa yadda tun farko aka yi cinikin saida kamfanonin samar da wutan lantarkin duk matsala ne a kasar na.

” Idan ba haka ba yaya za a ce wai an saida kamfanin ga ‘yan kasuwa sannan kuma gwamnati ta narka har naira Tiriliyan 1.7 cikin shekaru uku bayan kuma an saida kamfanin. Wannan babban abin tambaya ne.

” Ina rokon mutane da a dan dakata tukunna sai mun mika wa gwamnati rahoton binciken mu kafin idan akwai abin cewa sai a fito a yi magana.

” Kuma lallai shawarwarin da za mu bada ba zai yi wa wasu dadi ba, amma dai dole mu dauki wannan mataki idan muna so wuri irin haka ya gyaru sannan ya amfani mutanen Najeriya.

” Haka kuma idan za a fadi gaskiya, akwai akalla mutane miliyan 80 a kasar nan da basu samun wutan lantar ki kwata-kwata. Hakan ba za a bari ya ci gaba sannan kuma ace wai bayan an saida kamfanin wutan, gwamnati ta kashe naira Tiriliyan 1.7. Akwai abin lallai ayi zurfin tunani akai.

El-Rufai yayi wannan bayani ne a taron Kwamitin Inganta Tattalin Arzikin Kasa. Kamar yadda jaridar PremiumTimes ta fitar.

Masu Alaka

An fanso dan Majalissar jihar Kaduna awanni kadan bayan anyi garkuwa da shi

Dabo Online

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama

2020: Rikici ya barke a APC tsakanin Oshiomhole da Gwamnan jihar Edo akan fitar da ‘yan takara

Dabo Online

Zamu ciyo wa ‘yan Najeriya bashin dala Biliyan 1 domin inganta harkar noma -Nanono

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya amince da ginin sabuwar kwalejin ilimi a jihar Bauchi

Dabo Online

Next Level: Gwamnatin Tarayya ta aminta da fara aikin titin Jirgin Kasa na Ibadan-Kano

Dabo Online
UA-131299779-2