Farfesa Aliyu Danshehu Maiwada na jami’ar Bayero ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Farfesa Maiwada ya kasance tsohon malamin a bangaren Geography na jami’ar dake Kano.
‘Dan gidan mamacin, Abdullahi Aliyu Maiwada ne ya sanar da mutuwar mahaifin nashi a ranar Asabar.
Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un (إِنَّا لِلّهِ وَإِنَّـا إِلَيْهِ رَاجِعونَ) "Surely we belong to Allah and to Him shall we return".
— Abdullahi Aliyu Maiwada (@abdul_maiwada) May 17, 2020
This is to announce the demise of my Father (Aliyu Danshehu Maiwada), on 23 Ramadan 1441AH.
Cikin kasa da kwanaki 30, jihar Kano ta rasa Farfesoshi da dama. Sai dai duk da barkewa annobar Kwabid19, babu alakar mutuwarsu da cutar ta Kwabid19.
A wani labarin kuma za ku ji cewa gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje ya amince da bude masallatan Juma’a da kuma bayar da damar yin Sallar Idi duk da karin wa’adin dokar kulle da gwamnatin tarayya tayi.
