Yanzu-yanzu: Ganduje ya amince da bude masallatan Juma’a da Sallar Idi a Kano

dakikun karantawa
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da bude masallatan Juma’a a jihar Kano.

Haka zalika ya sanar karin ranar Juma’a daga cikin ranakun sassauta dokar kulle a jihar.

Ya bayyana haka ne a yau Litinin yayin jawabin yau da kullin na al’amuran Koronabairas a jihar da aka saba gabatarwa a fadar gwamnatin ta jihar Kano wanda limamai da malaman jihar suka halarta.

“Shugaban kasa ya kara rufe Kano sati biyu nan gaba. Amma an bamu awanni 12 domin ayi wasu harkoki na rayuwa.”

Gwamnan yace za a rika sassauta dokar a ranakun Juma’a da Alhamis daga 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma a bisa sharadan da aka gindaya.

“Ga kuma yanayin yadda yazo, saboda haka muka kafa wani kwamiti mu duba mu gani idan mun saukakawa al’umma ayi sallar Juma’a, ta ya zamu saka ka’idoji na kiwon lafiya domin mu ga yadda suma limama za suyi amfani da wannan dama su ga anyi amfani da wannan ka’idoji.”

“”Saboda haka, ina gani da tsari nagari da hadin kan malamai, mu bari ayi sallar Juma’a, sannan mu bari ayi Sallar Idi.

DABO FM ta tattaro cewar gwamnan yace dole ne al’umma su kiyaye dukkanin matakan kariya wadanda jami’an lafiya suka bayyana, wand yace gwamnati ta za ta aike da ‘yan Hisba tare da ‘yan agajin kungiyoyin musulmai domin su tabbatar da matakan.

“Tijjaniyya an samu ‘yan agaji guda 500, Kadiriyya 500 haka kuma Izala suma 500 ga kuma ‘yan Hisba.”

“Mun zauna da shugabannin Teloli, mun ce zamu basu kayan aiki  wanda su ma zasu samu aikin yi na yin safa ta baki.”

Haka zalika yace gwamnatin jihar ta kafa kwamitin kwamishinoni domin su jagoranci rarraba kayayyakin matakan kariya da gwamnatin jihar ta sanya ayi domin a bai wa  masallatai a fadin jihar.

Yace dole a tabbatar dukkanin wadanda zasu zo masallacin an basu takunkumin fuska domin kariyar kansu da sauran mutane.

Karin Labarai

Latest from Blog