(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Cibiyar IAR Ta Kammala Shirin Gabatar Da Irin Masara Mai Jure Fari Da Cututtuka.

dakikun karantawa

Cibiyar binciken aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (IAR) ta kammala gabatar da ingantaccen irin masara wanda ke maganin kwari tate da jure fari da sauran cututtuka da ke addabar masara a gona.

Jagoran tawagar masu binciken tare da gwajin Sabon irin masarar Farfesa Rabi’u Adamu ya yi bayyana cewa binciken da gwajin da suka gabatar na hadin gwiwa ne tsakanin cibiyarsu da (IAR) da kuma “Afrian Agricultural Foundation a karkashin “TELA Maize Pryat” inda suke aiwatar da gwajin a kasashen bakwai a nahiyar Afirka.

Farfesa Rabi’u Adamu ya ce “TELA maize prayat” ta samar da Sabon irin masara mai nagarata da kuma aukin tsaba.

A cewarsa manoma masara a Nijeriya nan da shekaru biyu masu zuwa su sa ran ganin masra mai inganci da auki a daukacin kasuwannin Nijeriya wadda manoma Nijeriya za su noma.

Ya ce gaba da cewa ita wannan sabuwar masarar za ta maye gurbin tsohuwar masara da muke da ita saboda yanayita da kuma aukin da ta ke da shi.

Farfesa Adamu ya ce Nijeriya ta kasance mamba ne a shekarar 2019 kuma an kaddamar da ita a nan Nijeriya a 2020.

Haka nan kuma cibiyar binciken aikin gona (IAR) ta sami izinin daga hukumar da ke kula da irin wannan aiki ta kasa (National Biosafety Management Agency (NBMA) dan gudanar da noman gwaji ta hanyar shuka irin mai lamba (Mon 89034) wadda ke magance kwari da sauran cututtuka tare da jure wa fari mai lamba (Mon 87460) wanda kuma aka tabbatar da cewa yana da jure fari kamar yadda ake bukata.

Farfesa Adamu ya ce da zarar an kammala gwajin kuma aka amince da sakamakon ta za a samar da irin ta yadda zai wadaci manoma su fara amfani da shi domin samun amfani mai yawa fiye da wanda suke samu a baya musamman manoman da yankunansu ke fuskantar barazanar fari a dalilin rashin ruwan sama wadatacce.

Jagorar tawagar masu binciken Farfesa Rabi’u Adamu ya ce sakamakon wucin gadi na nuni da irin nasarar da aka samu daga irin bincike da gwajin da aka gudanar a yanayi daban- daban kuma aka sami amfani nunkin abinda da aka saba sami a hekta daya .

Sai dai wani abin takaici inji Farfesa Rabi’u shi ne ba duka manoma ne za su iya jurewa ba amma sai ka ga a karshe manomi ya gudu ya bar gonarsa ga kwari su yi ta shagali.

Ya ce, anasa ran samun samfarin irin masaran a hannu a shekarar 2021,manoma kuma kuma da tunanin zai samar da sakamakon da ake bukata na kasan cewarsa sahun gaba a kasuwanni.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog