Jar Miya: Rarara ya gwangwaje AB Mai Shaddan Kannywood da motar miliyoyi

Karatun minti 1

Fitaccen mawakin siyasar, Dauda Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Rarara, ya bai wa ma shirin fina-finan Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda dankareriyar motar zamani, DABO FM ta tabbatar.

Rarara ya bai wa Mai shadda mota ta kamfanin Mercedes Benz, fara kirar Kompressor ta zamani da kudinta suka haura miliyan 1.5.

Ba wanne ne karon farko da mawakin yake babbar kyauta ba, a watan Yuni da ya gabata, DABO FM ta rawaici yadda Rarara ya bai wa mawaki Aminu Dumbulum kyautar mota da Naira miliyan 1.

Da yake tabbatar da lamarin, Abubakar Bashir Mai Shadda ya bayyana farin cikinsa bisa kyautar da mawakin ya yi masa tare da yin furucin, “Alhamdulillah Alhamdulillah, Rarara ina godiya. Allah Ya biya ka da Aljannah, Chairman.”

DABO FM ta lura da tambayar da jaruma Maryam Booth ta yi wa AB Mai Shadda bayan ya wallafa hotunan motar da, jarumar ta ce; Ya bamu Mota?, inda yayi mata martani da; ‘Eh Wallahi Blood.”

A wani labarin kuma, watanni da suka gabata ma dai mawaki Rarara ya bai wa mai wasan barkwanci a shafukan sada zumunta ‘Shagir-gir-Bau kyautar sabon babur na zamani.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog