(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ɗaliban Kwankwasiyya sun kamo hanyar dawowa Najeriya daga Indiya

Karatun minti 1
Daliban Kwankwasiyya (2019) - Hoto: DABO FM

Wasu daga cikin ɗaliban da gidauniyar Kwankwasiyya ta kai ƙasar Indiya domin yin digiri na biyu, sun kamo hanyarsu ta dawowa Najeriya bayan kammala karatunsu, DABO FM ta tabbatar.

Tin dai a ranar 25 ga watan Satumbar 2019, rukunin daliban farko da gidauniyar ta dauki nauyi su ka sauka a ƙasar Indiya domin fara karatu.

DABO FM ta tattara cewar wasu daga cikin daliban sun taso a daren jiya Juma’a daga filin sauka da tashin jirage na Indira Gandhi da ke birnin Delhi, babban birnin ƙasar.

Daliban za su fara yada zango a Hadaddiyar Daular Larabawa kafin sun karaso Najeriya, kamar yadda wani daga cikin daliban ya shaida wa DABO FM.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog