Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya naɗa sabbin shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya bayan ya amince da saukar tsofaffin.
Sabbin hafsoshin su ne;
Major-General Leo Irabor, a matsayin sabon Shugaban ma’aikatan tsaro.
Major-General I. Attahiru, a matsayin sabon Babban hafson Sojan Ƙ asa.
Rear Admiral A.Z Gambo, a matsayin sabon babban Hafson Sojan Ruwa.
Air-Vice Marshal I.O Amao, a matsayin sabon babban Hafson Sojan Sama.
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Buhari ya amince da ajiye aikin tsoffin hafsoshin tsaron Najeriya da su ka dade suna riƙe da muƙaman.