/

Mashiryan shirin Labarina sun fara daukar kashi na 3

Karatun minti 1

Masu shirya fitaccen shirinnan na Labarina sun sanar da fara ɗaukar cigaban shirin kashi na 3.

Babban mai bayar da umarni a shirin, Aminu Saira ne ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

Darktan ya ce nan ba da daɗewa ba, za zu sanar da masoyan shirin lokacin da zai riƙa zuwa garesu.

Ya ce; “Cikin yardar Ubangiji, mun fara ɗaukar shirin LABARINA mai dogon zango kashi na 3.

“In sha Allah ba da jimawa ba, za mu sanar da ku lokacin da za a dawo haska muku shi. Ku taya mu da addu’a.

Shi ma Nazifi Asnanic, daya daga cikin masu ɗauƙar nauyin shirin, ya nemi al’umma su taya su addu’a a kan shirin.

Labarina, shiri ne da ya samu karɓuwa wajen masoya fina-finan Hausa musamman gabannin fara sarara dokokin kullen Korona a Najeriya.

Masana na ganin shirin ya shiga jerin shaharareun fina-finan shekarar 2020.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog