(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Daliban Najeriya guda 5000 a Sudan suna cikin tashin hankali da matsi

dakikun karantawa

Biyo bayan juyin juya hali da al’ummar kasar Sudan sukayi domin samun chanji daga dadaddiyar gwamnatin shugaba Omar Al- Bashir.

Neman sauyin mulkin ya bar baya da kura a kasar a daidai lokacin da rahotanni suka bayyana cewa sojoji a kasar suna farwa masu zanga zangar bayan samun nasarar kifar da gwamnatin Al-Bashir.

Rahotanni daga kasar sunce zuwa yanzu an kashe kimanin mutane 500, an gefa mutane 40 cikin bahar maliya inda mutane 700 sukayi batan dabo tare da kame mutane 650.

DABO FM ta binciko cewa akwai daliban Najeriya 5000 da suke karatu a kasar Sudan bayan da jakadan Najeriya a kasar ya bayyana a wata hirarshi da jaridar Daily Trust.

Kama yanzu, sojojin kasar ta Sudan sun toshe harkokin sadarwa dama yanar gizo gizo a kasar, inda ya zamana cewa babu wani labari ko rahoto dake fitowa daga kasar zuwa yanzu.

Iyayen daliban Najeriya dake karatu a kasar ta Sudan sun koka kan yacce basa samun yin magana da yaransu dan sanin irin halin da suke ciki.

“Hakan na faruwa ne bisa katse yanar gizo gizo da sojojin Sudan sukayi.”

Sai dai jaridar Daily Trust ta rawaito ganawar ta da wata daliba data samu damar dawowa Najeriya bayan ta samu izinin fita daga kasar Sudan.

Hafsat, daliba dake karatun likitanci a wata jami’a dake babban birnin Khartoum ta bayyana irin tsanani da tashin hankali da daliban suke fuskanta a halin yanzu.

DABO FM ta binciko Hafsat tana cewa “Abinda yake faruwa a kasar Sudan, babu wanda zaiso abin ya same shi, kuma wannan shine abinda ban taba ganin irinshi ba.”

Hafsat ta bayyana cewa daliban sukanyi kwana da kwanaki babu abinci bisa rufewar kasuwanni da shagunan kayayyakin abinci.

Tace ko a karshen azumin watan ramadana, da kyar da kyar suke samun abincin bude baki, saboda ba shiga babu fita.

Ta bayyana cewa kafin lamarin yayi tsanani, sukan fita su taka a kasa saboda katse harkokin sufuri a kasar, su kanje je neman abincin da ake kayyade adadin da za’a siyar a ranar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog