INEC ta kwace takarda shaidar cin zabe daga ‘dan majalissar APC a jihar Ondo

Karatun minti 1

Biyo bayan hukunci da wata babbar Kotu tayi a jihar Ondo, hukumar zabe ta INEC ta kwace takardar shaidar cin zaben da ta baiwa Mr Sina Akinwuni na jami’iyyar APC, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalissar jiha na karamar hukumar Okitipupa.

Kotu ta umarci a kwace kujerar ne sakamakon tabbatar da rashin samun nasararshi a zaben fidda da aka gudanar a watan Oktobar 2018.

Kotu ta tabbatar da Mst James Ololade-Gbegudu na jami’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben biyo bayan samun tabbacin cewa shine ya lashe zaben fidda gwanin da jami’iyyar ta gudanar.

DABO FM ta tattaro cewa; tini INEC ta aikewa Mr Akinwumi da ya gaggauta barin zauren majalissar tare da sanarwar ta kwace takardar shaidar data bashi a farko.

Tini dai shugaban hukumar zabe ta INEC ya bawa Mr Gbegudu takardar shaidar lashe zabe a ofishinshi.

Cikakken bayanin yana zuwa…..

Karin Labarai

Sabbi daga Blog