/

Bidiyo: Matasa sun datse titin Kaduna-Abuja tare da cinna wuta, sunce ‘Sai Buhari yazo’

Karatun minti 1

Shashin Hausa na jaridar Premium Times ya rawaito cewa; “Matasan garin Azara dake kusa da Jere, jihar Kaduna sun datse hanyar Abuja zuwa Kaduna na tsawon awa uku sun ce sai Buhari ya zo da kansa za bu bari matafiya su wuce.

Wani matashi cikin fushi ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES da ya fada cikin wannan turmutsitsi cewa ‘yan sandan dake yin shinge a wannan gari ne suka kashe wani matashi sannan suka harbi daya a kafa.

” Kawai don sun nemi ya basu Naira 50 shi kuma ya hana kawai sai suka harbe shi sannan suka harbe na baya a kafa.

Matafiya da motoci sun fi dubu a wannan hanya kowa yayi cirko-cirko yana zura wa ikon Allah ido.

Su ko matasa suka harzuka suna ta kona tayoyi suna ihu suna dole sai Buhari da Buratai sun zo kafin su bari a wuce.

Wasu matafiya da hada da wakilin PREMIUM TIMES sai da suka yi kusan awa uku a tsaye kafin da taimakon Allah aka samu saukin abin.

‘Yan sanda da Dagacin wannan gari sune suka rika tausa hasalallun matasan kafin suka bari aka fara wuce da misalin 8:15 na dare.”

Premium Times Hausa

Kalli Bidiyo;

Bidiyo Mallakar Premium Times

Karin Labarai

Sabbi daga Blog