(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Firgici a Kano: Ana zargin ƴan sandan ‘Anti-Daba’ da kashe mutum 2 a Sharaɗa

dakikun karantawa

Harbin bindigar dai yayi sanadiyar mutuwar wani matashi mai suna Abubakar Isah, bayan da aka cakkakawa wani mai suna Ibrahim Sulaiman (Mainasara) wuƙa wanda shaidun gani da ido suka tabbatar ƴan Anti-Daba ne sukayi aika aikar sanadiyyar ƙin basu na goro.

Dabo FM ta rawaito dama dai sashen hukumar ƴan sandan ta Anti-Daba sun saba kai farmaki domin karbar na goro a wanda shaidun gani da ido suka tabbatar mana shine ya yi sanadiyar rasa ran waɗannan matasa a unguwar ta Sharaɗa.

Da muke zantawa da wanda bin ya faru a gabangaban sa, ya bayyana mana “A ranar Asabar ƴan Anti-Daban suka yi kokarin karbar na goro daga hannun matasan wanda sukayi ƙememe suka hana, hakan ya jawo hukumar tayi amfani da alburushi mai kisan faraɗɗaya akan matasan.”

“Abubakar Isah wanda alburushin ya same shi ya fadi ya mutu nan take, Ibrahim Sulaiman (Mainasara) wanda shi kuma suka daba masa wuka har sau biyu inda ya faɗi cikin jini, daga nan aka kaishi asibitin Murtala dake cikin kwaryar birni, inda shima bai kai labari ba.”

Duka mamatan biyu anyi jana’izar su a ranar Lahadi, wanda har zuwa yanzu da muke haɗa rahoton bamu samu ƙarin haske daga kakakin hukumar ƴan sanda ta jihar Kano ba. Kamar yadda SahelianTimes ta fitar.

Ko a satin daya gabata anyi irin wannan zargin wasu Ƴan Kwamati a unguwar Gwale wanda sukayi sanadiyar mutuwar wani matashi bayan sassara a cikin maƙabartar gwale kamar yanda ƴan uwan mamacin suka shaidawa Dabo FM, sai dai kuma sun zargi hukumar da juya maganar, wanda suka yi zargin har an saki wanda zuke zargi da aika aikar, nan gaba zamu kawo muku cikakken rahoton.

A watan da ya gabata na Oktoba shima dai irin wannan balahira ta faru a unguwar Kofar Mata wanda akayi irin wannan zargi na Ƴan Anti-Dabar sun kashe wani matashi wanda har saida ya kai da ƴan unguwar sun fito zanga zangar nuna bacin ran su.

Anan muke kira da mai girma kwamishinan ƴan sanda, Habu Sani (Kalam Wahid) domin tabbatar da bincike cikin adalci akan wannan zarge zarge da ake wa hukumar musamman shashin Anti-Daba da Ƴan Kwamiti, kaman yanda ya saba domin gudun faruwar haka anan gaba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog