Najeriya na da abubuwa da dama da za ta iya dogaro da su-Bashir Jamo

dakikun karantawa

Shugaban hukumar kula da hada-hadar jiragen ruwa ta kasa wato NIMASA Dakta Bashir Yusuf Jamo ya kwatanta kogin Kaduna a matsayin wata hanya na samar da aikin yi da kara farfado da darajar garin Kaduna. Ya ce tunda yanzu kasashe sun fara dawowa daga dogaro da man fetur, yanzu lokaci ya yi da za’a farka domin naimo hanyoyin mafita domin habbaka tattalin arziki ta kowacce fuska.

Dakta Jamo ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da ‘yan uwa da abokan arziki suka shirya masa na taya shi murna samun mukamin jagoran hukumar ta NIMASA, a Zariya ta Jihar Kaduna.

Ya ce, Najeriya na da abubuwa da dama da za ta iya dogaro da su ta fuskan bunkasa tattalin arzikin, kuma zuwa yanzu kasashe na harsashen daga nan zuwa shekarar 2030 dole ne a naimo wata hanya ta daban da za’a kara bunkasa tattalin arziki da harkar zuba jari musamman bangaren hasken rana da na lantarki wanda za’a iya amfani da su cikin motoci da sauran ababen amfani na yau da kullum.

Kuma kasa kamar Najeriya, lokaci ya yi da ya kamata a farka domin naimo mafita tun kafin wannan lokaci, Kuma daya daga cikin mafitan shi ne ruwan Teku, saboda yanayin albarkan da Allah ya aje a ciki sa. Kamar Gwal da Man fetur da sinadarin yin magunguna na cututtuka daban-daban, ballantana iskan ta da yake iya samar da wutan lantarki.

Kuma idan har kudancin Najeriya akwai ruwan Teku muma nan Arewa akwai tafkoki da dama da Allah ya huwace mu da shi kamar River Niger da River Kaduna.

Kuma duka abun da za’a iya samu a wancan ruwan za’a iya samu a namu nan na Arewa.

Dakta Bashir Jamo ya Kara da cewa, za’a samar da wuraren shakatawa daban-daban a gefen wannan ruwa da zai kawo cigaba sosai, kuma akwai sinadarai masu yawa da wannan ruwa ya kumsa.

Da ya juya ga manufar shirya taron da aka yi domin karrama shi kuwa, Dakta Bashir Yusuf Jamo, ya ce kowanne dan Adam na da wasu manufofi da yake son cimmawa a rayuwar sa, Kuma dole kowwa ya sanya tsoron Allah a tsarin rayuwar sa domin idan mutun baya ganin ka to Allah na ganin ka.
Kuma kusan wannan shi ne sirrin samun nasarar da ya samu har ta Kai shi ga matsayin da yake a yanzu.

Ya gode ma wanda suka shirya taron da manufar karrama shi, kuma ya yi fatan samun nasara mai dorewa a sauran rayuwa a gaba.

Alhaji Umar Sani wani makusanci ne ga Dakta Bashir Jamo, ya kwatanta shi a matsayin jagora na gari kuma nagartacce a dukkanin abubuwan da ya sa gaba, wanda ya ce kusan shi ne ma sirrin samun wannan nasara.
Kuma taro irin wannan na da muhinmanci musamman saboda addu’o’i na fatan Alheri da nasihohi da ake ma wanda aka shirya taron domin shi.

Ya gode ma kwamitin da suka shirya taron, kuma ya yi addu’an gamawa lafiya ga shi shugaban na NIMASA Dakta Bashir Yusuf Jamo.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog