Kano: Ɗan majalissar Takai da Sumaila zai ɗauki nauyin yi wa al’ummarsa rijistar CAC

Karatun minti 1

Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Takai da Sumaila ƙarkashin jam’iyyar APC, Honarabul Shamsuddeen Bello Dambazau, ya ce zai dauki nauyin yi wa al’ummar ƙaramar hukumar da yake wakilta rijistar kamfani da sana’o’i manya da ƙanana kyauta.

Majiyar Dabo FM ta bayyanar sanarwar ta fito ne ta hannun wani makusancin ga ɗan majalissar ka na kuma shugaban kamfanin hoto na Shakaka, Umar Faruq Musa ranar 27 ga Satumba.

Hukumar CAC dai ita ce wadda kamfanoni da masana’antu manya da ƙanana ke yin rijista da ita domin samun shaida a hukumance bisa kudin tsarin mulkin Najeriya.

Sanarwar ta fara da sallama, “Ina so nayi amfani da wannan dama wajen sanar da al’ummar  ƙananan hukumomin Takai da Sumaila cewa wanda yake da certificate na CAC ya turomun ni, Umar Faruk Musa Shakaka, ko Abubakar Ahmad Garba Kachako ko Sen Abdullahi Muhd Sumaila.  tare da bayanan sa.”

“Wanda kuma ba shi da shi,  akwai tsarin da ake bi, wato na yanar gizo ayi rijista ta naira 500, wanda za ka shiga shafin yanar gizo na hukunar yin rijistar kamfanoni da masana’antu manya da kanana, Corporate Affairs Commission, CAC.”

Shakaka ya kara da cewa “Sai ka dauki hoton fejin shaidar kayi sai ka turo mana, daga nan kuma za mu biya maka sauran dubu goman ta hannun Hon Shamsudeen Bello Dambazau, Dan Majalisa mai wakiltar Sumaila da Takai a Majalisar Tarayya.”

Hoto: Shakaka

Karin Labarai

Sabbi daga Blog