Sarautar Zazzau: El-Rufa’i ya yi fatali da sunayen da majalissar nadin Sarki ta aike masa

dakikun karantawa
El Rufa’i
Mallam Nasiru EL-Rufa'i - Gwamnan jihar Kaduna (APC)

Wasu rahotanni daga Jaridar yanar gizo ta Premium Times, sun bayyana cewa gwamna El- Rufai ya yi fatali da jerin sunayen da majalissar nadin Sarki ta aike masa.

Kazalika sun tabbatar da cewa gwamnan ba zai yi amfani da sunayen da majalissar ta aike masa ba.

Tin dai kwanaki 2 da suka wuce, majalissar nadin Sarkin Zazzau da ke da mutum biyar ta aike da sunayen mutane 3 masu zawarcin kujerar sarautar Zazzau.

Sun hada da Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu; Yariman Zazzau, Alhaji Mohammed Munir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris.

Masu nadin Sarkin ba su aike da sunan Ahmad Bamalli ba, wanda ake zargin cewa shi ne muradin gwamnatin jihar Kaduna.

Jaridar ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta sanya sunan Ahmad Bamalli a cikin masu zawarcin sarautar Sarkin Zazzau.

Zargin karbar na goro

Majiyoyin jaridar sun tabbatar da cewa gwamna Mallam Nasiru ya yi fatali da sunayen da majalissar nadin Sarkin ta aike masa tare da zarginsu da karbar cin hanci wajen tattara sunayen.

Wanda tace hakan yana daga cikin dalilin da ya sa gwamnan ya yi fatali da sunayen.

Tuni dai wani daga bangaren gwamnati wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan majalissar nadin Sarkin sun amsa karbar na goro daga wasu daga cikin masu neman sarautar.

“Tasirin abun ya zama babba wanda har gwamnatin ta samu wasu shaidun biyan kudi.” – cewar wani daga majiyar.

DABO FM ta tattara cewa gwamna El Rufa’i ya ce gwamnati ta tattara mutane 11 da suka nuna bukatar gadar kujerar wanda a cewar gwamnatin tuni da aike da sunayensu zuwa jami’an tsaro domin yin bincike.

Yau dai dai Marigayi Dr Shehu Idris ya shafe mako guda da rasuwa, ya rasu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog