Ina dana sanin shugabantar kwamitin da Buhari ya kafa kan binciken Magu -Salami

dakikun karantawa

Jastis Ayo Salami, shugaban kwamatin binciken rashawa da ake zargin dakactaccen shugaban riƙo na hukumar EFCC, Ibrahim Magu wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kafa ya yi dana sanin karbar shugabancin kwamitin.

Lauyoyin dake kare Magu ne suka bayyanawa majiyar mu ta Dabo FM jim kadan bayan wani zaman sirri da kwamitin ya yi wanda ba’a bari ƴan Jaridu sun shiga ba ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa.

An kafa kwamatin binciken wanda tsohon shugaban kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasa, Jastis Salamin ke shugabanta bayan Atoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami ya zargi dakataccen shugaban riƙon hukuma yaƙi da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu da rashawa, mai dokar bacci ya bige da gyangyaɗi, wanda hakan ya jawo dakatar da Magun.

Da suke tseguntawa Dabo FM, lauyoyin da suke kare Magu, Tosin Ojaoma da Zainab Abiola, sun bayyana cewa “Bayan fara zaman cike da dana sani, [Salami] ya dauko hankici yace, ina matuƙar dana sanin karbar wannan aiki.”

“Da muka tambaye shi ko saboda ba’a kama wanda muke karewa [Magu] da kowane laifi ba ne yasa ka ke faɗar haka, sai yaƙi bamu amsa, yace ina yin dana sani ne kawai.” Kamar yadda PremiumTimes ta fitar.

Shugaba Buhari dai ya kafa kwamatin binciken ne na fannin shari’a, ƙarƙashin dokar kotun Taraibuna (Cap T21, LFN, 2004), za kuma ayi binciken daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2020.

Tuni dai tin a watan Yuli aka chafke Ibrahim Magu wanda har saida ya yi kwanaki 4 da kulle cikin wajen tsare masu laifi na fadar shugaban ƙasa.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog