(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ganduje yayi alkawari mayar da karatun Firamare kyauta da daukar nauyin karatun masu bukata ta musamman

Karatun minti 1Gwamanan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin zata mayar da karatun firamare kyauta a jihar, tare da daukewa dukkanin masu bukata ta musamman nauyin kudaden makaranta na kowanne mataki.

A jawabin da gwamnan yayi jim kadana bayan shugaban jami’ar jihar,Mai shari’aNuradeen Sagir Umar, tare da mataimakinshi, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya alkauranta mayar da kokarin wajen tilastawa yara zuwa makaranta tare da saukake musu biyan kudin makarantar Firamare.

Gwamnan yace, gwamnatin zata duba wajen saukaka kudaden da daliban makarantun gaba da sakandire suke biya. Ya kuma ce zasu kara hubbasa wajen inganta fannin lafiya a jihar.

Ganduje dai yace gwamnatin ta shirya yakar matsalar rashin ruwa a jihar, ya ce gwamnatin zata kirkiri sabon kamfanin mai suna “Kano State Small Town Water Supply Agency” domin samar da ruwa a cikin kauyukan jihar ta Kano.

Ya kuma alkauranta bunkasa bangaren noma musamman ga kananan manoma masu karamin karfi.

Ganduje yace wannan salon gwamnatin tashi ta biyu, bazata lamunci cin hanci da rashawa ba, yace zai karawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar wajen gudanar da ayyukan ta da gaske.

Ya alkauranta shigo da duk wadanda zasu iya baiwa jihar Kano cigaba cikin gwamnati domin a hada karfi da karfe wajen ciyar da jihar gaba, ba tare da duban jami’iyyar ko siyasa ba.Karin Labarai

Sabbi daga Blog