Siyasa

NextLevel: Ganduje ya alkauranta kakkabe cin hanci da rashawa a jihar Kano

Gwamanan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin ta shirya tsaf wajen yakar cin hanci da rashawa a jihar ta Kano.

A jawabin da gwamnan yayi jim kadana bayan shugaban jami’ar jihar,Mai shari’aNuradeen Sagir Umar, tare da mataimakinshi, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya alkauranta mayar da kokarin wajen tilastawa yara zuwa makaranta tare da saukake musu biyan kudin makarantar Firamare.

Gwamnan yace, gwamnatin zata duba wajen saukaka kudaden da daliban makarantun gaba da sakandire suke biya. Ya kuma ce zasu kara hubbasa wajen inganta fannin lafiya a jihar.

Ganduje dai yace gwamnatin ta shirya yakar matsalar rashin ruwa a jihar, ya ce gwamnatin zata kirkiri sabon kamfanin mai suna “Kano State Small Town Water Supply Agency” domin samar da ruwa a cikin kauyukan jihar ta Kano.

Ya kuma alkauranta bunkasa bangaren noma musamman ga kananan manoma masu karamin karfi.

Ganduje yace wannan salon gwamnatin tashi ta biyu, bazata lamunci cin hanci da rashawa ba, yace zai karawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar wajen gudanar da ayyukan ta da gaske.

Ya alkauranta shigo da duk wadanda zasu iya baiwa jihar Kano cigaba cikin gwamnati domin a hada karfi da karfe wajen ciyar da jihar gaba, ba tare da duban jami’iyyar ko siyasa ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

An yaba kokarin Ganduje na karin Naira 600 akan sabon albashin ma’aikata

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Dabo Online

Ni ba sa’an Sunusi bane – Ganduje

Dabo Online

Kotun Koli: Farfaganda baza ta canza abinda Allah ya tsara ba -Abba ya yiwa Ganduje martani

Muhammad Isma’il Makama

Zuwan Buhari Kano: Barranta rashawa ko goyon bayanta?

Dabo Online
UA-131299779-2