(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Goggon biri ya hadiye miliyan 7 a gidan namun dajin jihar Kano?

dakikun karantawa

Al’ummar jihar Kano, sun koka kan yacce suka samu labari daga wasu jami’an dake kula da gidan namun daji dake jihar na wani goggon biri daya sace kudaden shiga gidan kimanin Naira Miliyan 7.

A ranar laraba ne shugaban tattara kudaden shiga gidan namun dajin ya bayyana cewa an samu salwantar naira miliyan 6 da dubu dari takwas da dubu ashirin na kudaden da aka tara a lokutan bikin sallah da mutane ke cikowar zuwa kallon namun dajin.

DABO FM ta rawaito Shugaban yace sun ajiye kudaden ne a inda suka saba ajiye, bayan cincirundon Jama’a ne aka nemi kudin aka rasa.

Sai dai gidan Rediyon Freedom dake jihar ya zanta da wani ma’aikacin gidan namin dajin wanda ya bukaci a sakaya sunanshi, ya bayyana cewa wani narkekn gwaggon biri ne ya lallabo a guje ya sace kudin.

Shashin BBC Pigdin ya rawaito cewa ta zanta da shugaban hukumar tattara kudade a gidan namin dajin yaki tabbatar ko share rahotan gidan rediyo Freedom inda yace ana gudanar da bincike ne akan lamarin.

“Ana bincike ne akan lamarin yanzu shiyasa bazance komai ba, manema labarai dayawa su nemi jin ta baki na, amma abinda zan tabbatar shine, lallai cewa kudaden sun bata.”

SUma a nasu bangaren, jami’an yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar al’amarin inda tina ma dai sukayi awon gaba da ma’aikatan bangaren kudi da sukayi aiki a ranar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Lallai abin ya faru, kudade sun bata a gidan Zoo na jihar Kano a lokacin bukukuwan Sallah, yanzu haka mun kame ma’aikatan gidan su 10 kuma tini muka danka su ga hukumar CID.” – DSP Abdullahi

Karin Labarai

Sabbi daga Blog