Siyasa

Kotun koli ta kwace kujerar Sanatan APC a jihar Niger

Labarin da ke shigowa daga kotun kolin Najeriya da duminsa na nuna cewa kotun a yau Juma’a, 14 ga Yunin 2019 ta kwace kujeran sanatan APC mai wakiltan jihar Neja ta gabas, David Umaru. Ta alanta Mohammad Sani Musa matsayin zakaran zaben.

Kotun kolin ta yi watsi da shari’ar kotun daukaka kara na ranar 8 ga Afrilu, 2019 wacce ta baiwa David Umaru, nasarar cin zaben fidda gwanin jam’iyyar a jihar Niger.

Kwamitin alkalai biyar da suka zauna kan al’amarin karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Muhammad, sun yi ittifakin cewa jawaban lauyan Mohammad Sani, Wole Olanipekun, gaskiya ne kuma lallai shi yayi nasara a zaben fidda gwani.

Saboda haka, ta tabbatar da shari’ar da Alkaliyar babban kotun tarayya dake Abuja, Folashe Giwa-Ogunbanjo, na cewa Musa ne sahihin dan takarar jam’iyyar APC a zaben.

Legit Hausa

Karin Labarai

Masu Alaka

Kotu ta watsar da bukatar Atiku na bincikar kundin tattara sakamakon zaben 2019 daga INEC

Dabo Online

Kotu ta daure babban jami’in INEC shekaru 6 bisa hannu a cikin karbar cin hancin miliyan 45

Dabo Online

Taraba: Yawon kamfen a jirgin kwale-kwale

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Baza mu yarda da hukuncin kisa ba, zamu daukaka kara -Lauyoyin Maryam Sanda

Muhammad Isma’il Makama

APC tayi rashin nasara bayan kotu ta tabbatar da Darius Ishiaku na PDP a matsayin halastaccen gwamnan Taraba

Dabo Online

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2