Sadiya Umar Faruk
Labarai

Gwamnati ba zata tallafawa wadanda suke da sama da N5000 a asusun banki ba – Sadiya Faruk

Gwamnatin tarayya tace ba zata kayan tallafinta bazai kai zuwa ga duk wanda ya mallaki sama da N5000 a asusun banki ba.

Gwannatin tace za tayi amfani da layukan wajen domin gano masu bukata ta hanyar lura da wadanda suke sanya katin N100 ko na kasa da haka a wayoyinsu.

Ministar ayyukan jinkai da bala’i, Haj Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana haka yayin da take ganawa da manema labarai a yau Laraba.

Haka zalika tace gwamnatin tarayya za ta shigo da gwamnatocin jihohin cikin shirin da take yi da taimakawa mabukata a wannan lokaci da aka sanya dokar hana fita a sassan Najeriya.

DABO FM ta tattara cewar Haj Sadiya tace gwamnati ta na da hanyoyi 3 da zata bi wajen nemo mabukata domin ta basu kayayyakin rage radadin zaman gida.

“Muna da hanyoyi guda 3 da zamu yi amfani da su. Zamu yi amfani da hanyar kundin bayanai da muke dashi.”

“Na biyu, zamu yi amfani da hanyar lambar BVN wajen nemo mabuta, wadanda kudin asusunsu bai wuce N5000 ba.”

“Na uku shine zamu yi amfani da layukan waya domin binciko wadannan mabukata, wadanda suke saka katin N100 ko kasa da haka.”

“Da zarar mun kammala tattaro mutanen, zamu fara rabon kayyakin.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Mutane 148 sun sake kamuwa da Kwabid-19, 32 a Kano, 14 a Zamfara da sauransu

Dabo Online

Yanzu yanzu: An samu karin mutum 20 masu dauke da Coronavirus, jumilla 131 a Najeriya

Dabo Online

Covid-19: Matakan da gwamnatin Kaduna ta dauka shi ne mafita – Dakta Hussaina Adamu

Mu’azu A. Albarkawa

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Aisha Muhammad

Zamu aiko muku da kayyakin da zasu rage radadin zaman gida – Buhari

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun kamu da Koronabairas yau a jihar Kano, jumillar 313

Dabo Online
UA-131299779-2