Gwamnatin jihar Kano ta amince da fara biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ma’aikatan jihar daga watan Disambar 2019.
Ana sa ran ma’aikatan jihar zasu fara karbar albashin a tsakanun ranakun Litinin da Talata.
Hakazalika gwamnati ta bayyana biyan bashin bashin cikon kudin tin daga watan Afirilun da karin kudin ya zama doka, sai dai Gwamnatin tace zata biya ne kadan-kadan.
DABO FM ta tattara cewa hakan na zuwa ne bayan cimma yarjejeniya tsakanin tsagin gwamnatin jihar da kungiyar kwadago reshen jihar Kano.
A wata sanarwar da jami’an hulda da jama’a na gwamnati Kano, kwamitin tattauna biyan albashin, Kwamared Magaji Muhammad Inuwa, ya sanya wa hannu, yace tsagin gwamnati da na ma’aikata sun amince da yarjejeniyar fara biyan albashin a ranar 19 ga watan Disamba, kamar yacce Solacebase.com ta tabbatar.
Kwamitin ya yabawa gwamnati jihar kokarinta na tabbatar da fara biyan albashin daga watan Disamba tare da biyan bashin ragowar kudin tin na watan Afirilu.
Haka zalika ya kuma yi kira ga ma’aikata da su cigana da tsage dantse wajen yin aiki tukuru.
Ga yacce jadawajin biyan albashin zai kasance; Daga Solacebase.com
RUKUNI NA 1
CONPSSS
GL 01 – 06 70%
GL 07 30%
GL 08 18%
GL 09 14%
GL 10 – 14 12%
GL 15 – 17 8%
RUKUNI NA 2
CONMESS
CM 01 – 04 5%
CM 05 – 07 4%
CONHESS
CH 01 – 04 29%
CH 05 22%
CH 06 14%
CH 07 9%
CH 08 7%
CH 09 6%
CH 10 – 11 5%
CH 12 – 15 4%
RUKUNI NA 3
CONPCASS
CONP 01 6%
CONP 02 – 06 5%
CONP 07 – 09 4%
CONTEDISS
CONT 01 25.31%
CONT 02 25%
CONT 03 24%
C0NT 04 21%
CONT 05 17%
CONT 06 10%
CONT 07 6%
C0NT 08 – 12 5%
CONT 13 – 15 4%
RUKUNI NA 4
CONJUSS
GL 01 – 05 63%
GL 06 50%
GL 07 23%
GL 08 16%
GL 09 14%
GL 10 11%
GL 12 10%
GL 13 9%
GL 14 8%
GL 15 – 17 6%
