//
Wednesday, April 1

Jerin jihohi 18 da basu da shirin fara biyan albashin N30,000

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Duk da wa’adin ranar 31 ga watan Disambar 2019 da kungiyar Kwadago ta baiwa Gwamnonin Najeriya akan biyan sabon albashin N30,000, wasu daga cikin jihohi basu da shirin fara biyan albashin.

DABO FM ta tattaro adadin jihohi da basu fara shirin biyan albashin ba, domin gwamnatin jihar da kungiyar kwadago ta jihar basu zauna akan shirin tattaunawa biyan albashin ba.

Gwamnatocin jihohi 18 ne basu kafa kwamitocin tattaunawa tsakanin tsagin gwamnatin da kungiyar kwadagon ba.

Johohin sun hada jihar Anambra, Bauchi, Benue, Cross Rivers, Delta, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Kogi, Kwara, Nassarawa, Ogun, Osun, Oyo, Plateau, Rivers da jihar Yobe.

Masu Alaƙa  Yanzu Yanzu: Gwamnan Bauchi ya bada umarnin biyan sabon albashi na N30,000

Haka zalika jihohi 12 sun kammala kafa kwamitin tattaunawa da kungiyar Kwadago wadanda a ciki jihohi irinsu Kano, sun amince da fara biyan sabon albashi a watan Disamba.

Jihohin sun hada da; Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, Borno, Ebonyi, Edo, Kano, Katsina, Niger, Ondo, Sokoto da jihar Zamfara.

Tini jihohin Adamawa, Jigawa, Kaduna, Kebbi da jihar Legas suka fara biyan albashin mafi karanci na N30,000.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020