Majalissar zartarwar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 2.543 domin gina sabbin asibitoci da gyaran kananan asibotici dake yankin sabbin masaratun kano na Bichi, Gaya, Rano da Karaye.
Mallam Muhammad Garba, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, shi ne ya bayyanawa manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalissar zartarwar jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana cewa aikin zai kunshi ginin sashin bayar da agajin gaggawa da hadura, ginin sashen gadaje guda 22, sashin kula da Ido, hakori da kashi tare da inin dakunan gwaje-gwaje, sashin ajiyar gawa a kowacce cibiyar kula da lafiya.
DABO FM ta tattaro cewa gine-gine sun hada da ginin sabbin tituna mahada da asibitoci, Tankunan ruwa da rijiyar burtsatse.
Haka zalika, kwamishinan ya tabbatar da gyaran Ofisohin cibiyoyin lafiya, sashin kula da yara, sashin kula da hadura, dakunan gwaje-gwaje, sashin kwanciyar Maza da Mata, sashin karbar haihuwa, dakunan karbar Magani, sashin dafa abinci, sashin daukar hoton ‘X-Ray’ da dakunan yin tiyata.
Kwamishinan ya bayyan cewa Majalissar zartawar ta kara amincewa da samar da kayayyakin aiki a cibiyar kula da cutar kansa a kan kudi na Naira biliyan 4,238,855,671.91.
Haka zalika majalissar zartarwar ta amince da ginin sabuwar makarantar kwana ta Kimiyya da Fasaha ‘yan mata a garin Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa akan kudi na Naira miliyan 165,244,821.1
