(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnatin jihar Niger zata kashe Naira Biliyan 3.2 a gyaran Gidan Gwamnati

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Niger tace shirin da take na gyaran gidan Gwamnati zai lakume Naira biliyan 3.2.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Kwamishinan aikace aikace na jihar ta Niger ya bayyana haka a wani taron manema labarai  a jiya Alhamis.

Yace sun raba aikin ne kashi biyu, kuma tini dai kashin farko na aikin wanda aka riga aka kammala, ya lashe Naira biliyan 2.1, daya kason wanda yanzu za’a fitar da kwangilar akan Naira biliyan 1.6.

Ya kara da cewa, kashi na farko da aka kammala, shine ya hada da gyaran gidan baki daya, saka kofofi, katange gidan da kewaye, da kuma gyaran babbar kofar shida gidan.

A inda kashi na biyun kuma zai kunshi saka gadaje da dakunan kwana dana baki, ginawa da kuma gyaran Tafkin Wanka (Swimming Pool) da sauran abubuwan morewa.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog