Zaben Kano: Tsaka mai Wuya ga Jami’iyya Mai Mulki, Daga Umar Aliyu Fagge

dakikun karantawa

Ga duk mutumin da yake bibiyar al’amuran siyasa a Najeriya, yana da masaniya akan zaben Gwamnoni da na yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 9/3/2019.

A lokacin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana zaben wasu jihohi a matsayin wanda bai kammala ba wato “Inconclusive”, a cikin su har da Jihar Kano, Bauchi, Sokoto da fulato.

Hukumar zaben ta fidda ranar 23/3/2019 domin kammala sauran zaben mussaman inda aka samu korafi da sauran kunji kunji, yanzu haka kwana daya ne ya rage domin aiwatar da wannan zaben a jihohin da abin ya shafa.

Kowane bangaren siyasa yana yin shiri iya nashi domin samun nasara.

Hankalin duniya yafi karkata izuwa jihohi kamar Kano da Bauchi, domin ana ganin guri ne da shugaba Buhari yake da rinjayen magoya baya, amma sakamakon wani dalili alummar jihohin sun amince su juyawa jami’iyya mai ci baya tare da dauko dan takarar da yafi na jam’iyyar ta APC cancanta.

A nan kano dai dan takarar jam’iyyar hammaya ne ke kan gaba da kuri’u sama da dubu ashirin da shida 26000^, a inda Gwamna mai ci yake neman warware wannan tazara a zaben da za a gudanar na ranar Asabar mai

Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya Gwamnati mai ci zata biya bashin kuri’un da ake binta?

Da dukkan alamu nazarin masu ilimin siyasa na nuni da cewa zabi biyu ne kacal ya ragewa Gwamnati a zaben da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa, gasu kamar haka:

  • Idan Gwamnati ta shiga za6e na tsakani da Allah zata sha mamaki, domin alamu na nuni da cewa masu za6e basa goyon bayan Gwamnatin saboda dalilan gazawar Gwamnati a fili wanda ya bayu ga jama’a su nemi canji a kakar za6en da muke ciki.

  • Za6i na biyu shi, ne Gwamnati zata iya yin amfani da karfin mulki gurin siyan kuri’un wasu marasa kishi tare da daukar nauyin yan bangar siyasa domin tayar da tarzoma a gurin da suke ganin ba zasu samu nasara ba. Wanda hakan zai bawa hukumar za6e damar soke za6en wasu akwatunan tare da komawa gurin sakamakon farko domin ayyana mutumin da yayi nasara, dama jam’iyyar adawa ta biyo jam’iyya mai mulki bashin kuri’u dubu ashirin da shida da yan kai.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog