Siyasar Kano sai Kano: Daga gobe kowa ya cire jar hula sai bayan zabe – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Madugun tafiyar darikar Kwankwasiyya yayi kira ga magoya bayan tafiyar ta Kwankwasiyya dasu cire jar hula har sai bayan zabe.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira daya gabatar a daren Alhamis, a gidan Rediyon Wazobia dake garin Kano.

“Daga gobe, kowa ya cire jar hula sai bayan zabe.”

Sai dai al’umma sun fara cewa ko menene dalilin daya sa Kwankwaso ya baiwa Kwankwasawa wannan umarni?

Mun tattauna da wasu wadansu magoya bayan tafiyar ta Kwankwasiyya, inda suka bayyana mana cewa sun samu labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta dauko wasu matasa tare da raba musu makamai da ja-jayen huluna domin su tada hargitsi a wuraren zabe.

Masu Alaƙa  Biyan Albashi: Bance kar a biya ma'aikata N30,000 ba - Kwankwaso

Za dai a gudanar da karashen zaben gwamnan da hukumar INEC ta kira wanda bai kammala ba a ranar 23 ga watan Maris, shekarar 2019.

 

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: