(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnatin Kano ta tabbatar da sabon mukamin Engr Mu’azu Magaji

Karatun minti 1
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da baiwa tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje, Engr Mu’azu Magaji mukami, kamar yadda DABO FM ta rawaito.

Cikin takardar kama aiki da ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ya aike wa Engr Mu’azu, takarda mai lamba SSG/REPA/S/F/59/1 ta ce gwamnatin ta nada shi a matsayin Shugaban Kwamitin da zai jagoranci aiki samar da Bututun Iskar Gas.

“Gwamnan Dr Abdullahi Ganduje ya amince da kafa Kwamitin na tabbatar da aikin sanar da bututun iskar Gas da masana’antun Gas na jihar Kano wanda zai yi aiki da NNPC.”

“Ina sanar da cewa an amince da nada ka a matsayin shugaban Kwamitin.”

An nada Alhaji Kabiru Musa Adamu, shugaban Kungiyar masu kera kayayyaki ta Najeriya reshen Sharada/Chalawa, wanda zai kasance a matsayin mataimakin shugaba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog