Batanci ga Annabi: An yi kira da Ganduje ya canza wa titin ‘France Road’ suna

Karatun minti 1

Anyi kira da gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya canza wa titi mai dauke da sunan ƙasar Faransa suna dake jihar Kano domin Allah-wadai da goyon bayan batancin da shugaban ƙasar, Emmanuel Macron ya nuna.

Dabo FM ta tattara cewa wannan na zuwa ne bayan kiraye kiraye na ƙauracewa kasar ta Faransa biyo bayan wani zene da jaridar ‘Charlie Hebdo‘ tayi akan fiyayyen halitta SAW, wanda saida ya jawo Faransa ta rufe ofishin jakadancin ta a ƙasashe fiye da 20 a fadin Duniya sakamakon firgice.

Kiran yazo daga wani matashi dan asalin jihar Kano, Sadiq Gentle wanda ya bayyana “Ganduje a dubi Allah a canjawa titin France Road suna zuwa Islam Road.”

Kwanaki kaɗan da suka wuce anyi irin wannan kiran akan gwamnan Kano ya kori sabon kocin kungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars, Emmanuel Leonel Soccoia wanda ɗan kasar Faransan ne.

Kiran yazo ne daga marubuciya kuma gogaggiyar ƴar jarida, Hadiza Balanti.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog