Daliba ‘yar Najeriya ‘Rukayya Nata’ala’ ta rasu a kasar Indiya

Karatun minti 1
Marigayiya Rukayya Nata'ala

Wata daliba yar Najeriya mai suna Rukayya Nata’ala, ta rasu jiya Laraba 28 ga Oktoba a  kasar Indiya, bayan fama da rashin lafiya, DABO FM ta tabbatar.

Dalibar da ta rasu a asibitin Jami’ar Sharda dake jihar Uttar Pradesh a arewacin kasar ta Indiya, daliba ce dake ajin karshe a karatun da take yi na Digiri na 2 a fannin Kimiyyar Kwamfuta a jami’ar Sharda.

CIkin wata sanarwa da Kungiyar Dalibain Afrika dake karatu a kasar Indiya ‘AASI’ ta aike wa DABO FM, ta ce za a yi jana’izar Rukayya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yau Alhamis da misalin karfe 1 na rana a agogon kasar Indiya (8:30 agogon Najeriya).

“Muna fatan Allah Ya jikanta ya kuma yafe mata dukkanin kurakurenta Ya kuma sanya ta a Aljanna Firdausi. Muna rokon Allah Ya ba wa dangi da abokanta dangana da hakurin wannan rashin da suka yi.”

“Za a yi jana’izar yau da misalin karfe 1 a Nazamudden dake babban birnin New Delhi.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog