Labarai

Gwamnatin Najeriya zata fara cin tarar naira miliyan 5 ga masu yada labaran karya a yanar gizo

Ministan yada labarai na Najeriya Lai Mohammed, ya shaida cewar mahukuntan kasa sun amince da a sake duba wata tsohuwar doka, da ta bada izinin ci tarar naira miliyan biyar ga duk wata kafa da ta yada labaran kanzon kurege, haddasa kiyayya, rashin jituwa da dai makamantansu.

Ministan ya bayyana haka ne a wata ganawa ta musamman da manema labarai, bayan kaddamar da wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Armstrong Idachaba, da zai tabbatar da gyare-gyare a hukumar kula da kafofin yada labarai ta kasa, inda ba za a bari siyasa ta shiga harkokin hukumar ba.

Lai Mohammaed ya ce babu gwamnatin da ta san abinda ta ke yi, za ta amince da wannan dabi’un da zasu iya kawo rashin jituwa a tsakanin al’umma, saboda haka gwamnati za ta yaki kowace kafa ce, ko ta wacce hanya da doka ta bada izinin yi.

Matakin dai, yayi ma Ciroman Bakan Daura dadi, inda yayi tsokaci da cewa, Najeriya tana da jami’an tsaro kwararru da za su iya kama duk wanda yayi irin wannan aika-aikar a kafafen yanar gizo.

Karin Labarai

Masu Alaka

Buhari ya amince da ginin sabuwar kwalejin ilimi a jihar Bauchi

Dabo Online

Babu wadanda suke iya saka katin N100 a tallafin gwamnati – Minista

Dabo Online

N-Power: Gwamnatin tarayya ta dauki mutane 1,350 aiki a Ribas

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin tarayya za ta cigaba da yin ayyukan raya kasa da kudin ‘Yan Fansho – Aliero

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin sakin Sambo Dasuki da Sawore

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin tarayya za ta soke shirin Talabijin na ‘#BBNaija’

Dabo Online
UA-131299779-2