Shugaba Buhari bai so bada umarnin rufe Iyakokin Najeriya ba – Ministar Kudi

Babbar Ministar Kudade ta Najeriya, Zainab Ahmad, ta bayyana cewa; rufe iyakoki ta Najeriya tayi, ya jefa kasashen dake makwaftaka da ita cikin halin kunchi.

DABO FM ta tattaro cewar; Ministar ta bayyana haka ne yayin da take magana da manema labarai a birnin Washington na kasar Amurka kamar yacce Jaridar Premium Times ta rawaito.

Ta kuma kara da cewa; shugaba Muhammadu Buharu, bai so ya bayar da umarnin rufe iyakokin ba, kasancewar rufewar zata janyowa makwaftan Najeriya shiga cikin wani hali na rashin dadi.

“Shugaba Muhammadu Buhari bai so bada umarnin rufe kan iyakokin kasashen ba, saboda halin kuncin matsin tattalin arzikin da zai jefa wadannan kasashe.”

Zainab, ta kara bayyana rashin kiyaye dokokin Najeriya da kasashen dake makwaftaka da kasar basu yi ba, hakan ya kara zamewa Najeriya tilas wajen rufe iyakokin domin habbataka tattalin arzikin kasar.

Masu Alaƙa  Ba’a kama ‘Yan Arewa 123 da aka tsare a jihar Legas da miyagun makamai ba -‘Yan Sanda

“Babu shakka rufe iyakokin Najeriya zai shafi tallatin arzikin kasasehen da muke da makwaftaka.

Ministar tayi nuni kan cewa; budewar iyakar Najeriya sakaka yasa maimakon a rika sauke kayayyaki ta tashoshin Ruwan Najeriya, sai a karkata a sauke a tashoshin Ruwan makwaftan kasashen, wanda hakan Najeriya bata karuwa da komai.

“Kokarin da muka yi na rufe kan iyakar mu da makwaftan kasashen, mun yi ne domin a rika sauke kaya a tashoshin jiragen ruwan mu, wadanda ake karkatarwa ana saukewa a tashoshin jiragen ruwan wadancan kasashe.

“Wadannan kayayyaki da ake saukewa kamata ya yi a rika sauke su a kwantina a tashoshin ruwan Najeriya, kwastan su duba, su caje su haraji, su biya.

Masu Alaƙa  Zabe a Tuwita tsakanin kwalliyar daliban Kano da Borno a bikin Satin Al’adu na Jami’ar ABU Zaria

“Amma ba haka ake yi ba, sai su bari a can a bude kwantina, a rika kwasar kayayyakin kunshi-kunshi ana sumogal din su a Najeriya ta cikin barauniyar hanyar kan iyakokin mu.” a cewar Ministar

“Idan ba haka ba kuwa, to kananan masana’antun mu ne za su fi tagayyara sosai.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.