Labarai

Dalibai sun hada N495,000 don jinyar d’an uwansu Dalibi

Daliban Jami’ar Ilorin ta jihar Kwara, sun hada Naira Dubu Dari Hudu da Casa’in da Biyar (495,000) don ai wa dalibi mai suna Abdulbasir Oladele aikin Tiyata a Idanunsa.

Wannan sanarwa tana kumshe ne cikin mujallar Jami’ar Ilorin da ta fitar a ranar Litinin, in da ta bayyana cewa wannan Dalibi yana fama da matsalar Ido tun a watan Janairu 2019.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Dalibin ya fara karbar magani ne a Asibitin koyarwa na. Jami’ar ta olorin tun da farko, kafin daga bisani a tura shi Asibitin masu lalurar idanu dake Birnin Ikko.

Mujallar ta ce dalibin yana matakin kararu na 400 ne, kuma ya fuskanci aiki har sau Biyu a idonsa na barin Dama.

Sanarwa ta ce aikin dai za a yi shi ne a kan kudi Naira Miliyan Daya da Dubu Dari Uku da Casa’in da Biyar (1,395,000), wanda shi kuma iya Naira Dubu Dari tara 900,000 ya iya samu.

Saboda haka majinyaci ya bukaci cikon Naira 495,000 domin kammala aiki karshe, wanda yake shi ne mataki na karshe a aikin dama, wanda sashin lura da Daliban makarantar yayi wannan hubbusa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Bayan rahotan Dabo FM, wata gidauniya za ta kai dauki zuwa Makarantar Firamare ta garin Garo

Raihana Musa

Babu wadanda suke iya saka katin N100 a tallafin gwamnati – Minista

Dabo Online

Attajirar Najeriya ta bawa Najeriya tallafin Naira biliyan 1, zata rabawa Zaurawa da Marayu N25,000

Dabo Online

Mudassir & Brothers ya rarraba tulin buhuhunan shinkafa a Kano

Dabo Online

Buhari ya bada kyautar magani, gidan sauro, kayyakin gwaje-gwaje da dala 500,000 ga kasar Malawi.

Dabo Online
UA-131299779-2