Haɗarin addinantar da siyasar zamani – Tare da Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Taskar Malamai: Hadarin addinantar da siyasar zamani – Tare da Sheikh Hamza Uba Kabawa, Babban limamin masallacin Juma’a na Bello Road.

A wannan siyasar da muke ciki babu irin abin da talaka bai ji ba na yabo ko sukan wani bangare. Dukkan bangarorin masu fada a ji sun taka irin rawarsu.
Tun daga kan Malaman Addini, Furufesoshi da Malaman Jami”a, Kungiyoyi da yan fafutuka ( activists), yan siyasa masu karajin chanji da lauyuyi yan gwagwarmaya.
Kowa ya baje kolinsa a bangarensa ya fadi harsashensa. Duk da nufin samawa talakka yanci, walwala, saukin rayuwa da ci gaba.
Ba wannan ne matsalar ba. Babbar matsalar ita ce lokacin da aka wayi gari wadannan bangarori sun yi shiru a lokacin da ake gasawa alumma azaba kala kala.
Mafi muni kuma shi ne yayin da aka wayi gari mutanen dake karajin Jihadi da chanji da yakar zalunci karami dun koma suna suna goyon bayan babban zalunci.
Malamai masu da awar a fita a yi jihadin siyasa sun yi shiru.
Wasu sun koma kwatance da misalai.
Wasu kuma sun shige tsundum da su ake damawa.
Ina zaton daga Bakara zuwa Nasi babu ayar da ba a kawo ba don jan hankalin talakka ya fita ya kwaci yancinsa.
Hadisai kuwa da Usulu da Tarihin gwagwarmar magabata dabam dabam kan kwatar yanci da kawar da zalunci, babu irin wanda ba a kawo.
An shirya lakcoci da tarurruka iri iri duk dan talakka ya fita ya nemi yanci.
Amma bayan talakka ya sauke nauyin dake kansa. Sai aka wayi gari talakka ya samu kansa a cikin sabuwar bautar da ta fi ta da.
Ya samu kansa cikin sabon tsananin da zaluncin da ya gujewa.
Amma a maimakon a ji sautin jihadin siyasa daga bakin irin wadancan malamai da yan gwagwarmaya ,sai ake jin sautin siyasar hakurtatwa da danna kirji.
Siyasar jihadi ta koma Siyasar danna kirji.
An daina karanto ayoyin jihadi sai ayoyin hakuri da yarda da kaddara da fawwalawa Allah komai. Wadannan abubuwan ba laifi ba ne, amma idan an sanya du a muhallinsu da bigiren da ya dace.
Abu mafi muni ma shi ne inda aka dinga kafirta juna saboda sabani na siyasa.
Aka addinantar da wasu jam’iyyun wasu kuma aka kafirta su.
Aka musuluntar da wasu yan takarar wasu kuma aka kafirta su.
Aka shiga rigar addini don cimma manufa ta siyasa.
Aka kulla soyayya da gaba akan siyasa.
Aka halatta cin mutuncin kowa saboda siyasa.
Amma ba a yi nisa ba sai aka wayi gari wadanda akewa kallon kafirai ko azzalumai, sai aka ga ashe salihai in an kwatantasu da wadanda a da akewa kallon imani da nagarta.
Jam”iyyar da a da akewa kallon azzaluma, sai aka ga ashe tafi tausayi duk da irin zaluncinta.
To abin tambaya anan shu ne ayoyin Alkuranin ne ba dai dai ba ko kuwa ana yin amfani da su ne a inda ba muhallinsu ba ?
Tuni masana da hangen nesa suka nuna cewa bai dace a mayar da makarantu, majalisai da mimbarin masallatai wajen kamfen din siyasa ko tallan dan takara ba.
Bamu kai wannan wayewar da ci gaban ba. Kuma tsarin siyasar mu cike yake da matsala.
Amma wasu malaman suka nuna atafau cewa siyasa ma ta malamai ce , su ne da ita. To yanzu siyasa ta kai su rami sun rasa yadda zasu yi.
Wasu sun yi shiru. Wasu sun dan ce wani abu gudun kada talakawa su zage su. Wasu sun koma bayar da hakuri.
Wasu sun koma bayar misalai da kwatance.
Wasu cewa suke duk da haka akwai dam canji.
Wasu sun koma kare kansu cewa , da kyakkyawar niyya suka yi .
Wasu kuwa da su ake damawa babu damar magana.
Shawara ta a karshe ita ce malamai su sake lale, a canja tsari.
A kula da addini a siyasa kada a addinantar da siyasa.
Siyasar Annabawa dabam. Siyasar Demokaradiyya dabam.
Siyasar addini dukkaninnta gaskiya kuma cike take da adalci, kasantuwarta daga Allah.
Siyasar Demokaaradiyya kuwa cike take da son zuciya, danniya da zalunci, saboda tsarin dan Adam ne.
Manufa ta gyara dace na yana ga Allah.
Abu Abdullahi.
Hamza Uba Kabawa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog