Majalissar Dokoki ta jihar Kano ta amince da yi wa dokar Majalissar Sarakunan jihar Kano kwaskwarima.
Majalissar ta amince da kudurin gwamnati na nada sarkin Kano a matsayin shugaban majalissar Sarakunan jihar guda biyar.
Majalissar ta hannun shugaban masu rinjaye, Kabiru Hassan Dashe ta ce ta nada Sarkin Kano a matsayin shugaban majalissar sarakuna bisa cewa Kano ta fi sauran masarautun jihar guda biyar tarihi da shahara.
Tin da fari dai gwamnatin jihar Kano ta sanya matakin yin kama-kama da shugancin majalissar Sarakunan inda shugabancin majalissar zai rika zagawa tsakanin manyan sarakuna biyar na jihar duk bayan shekaru 2.
Kazalika majalissar ta amince da karin adadi na masu zaben Sarki daga hudu zuwa biyar a kowacce masarautar jihar.
Duka wannan na cikin sauye-sauyen da Majalisar Dokoki ta yi wa dokar masarautun ta jihar Kano ta 2019 sakamakon ƙudirin da gwamna ya aike mata.